Hukumar ICPC zata kwace wasu kadarorin iyalan 'Yar'adua a Abuja

Hukumar ICPC zata kwace wasu kadarorin iyalan 'Yar'adua a Abuja

Hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu laifuka da suka jibanci damfara watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPS) ta shirya kwace wasu filaye da gine-gine da suka kai darajar Naira biliyan 4.8 daga kamfanoni akalla 30.

Hukumar ta ICPC ta ce za ta kwace kadarorin ne daga hannun masu su saboda karar da aka kai masu na kin biyan harajin da ya kamata su biya na tsawon lokaci kamar dai yadda doka ta tanada.

Hukumar ICPC zata kwace wasu kadarorin iyalan 'Yar'adua a Abuja
Hukumar ICPC zata kwace wasu kadarorin iyalan 'Yar'adua a Abuja
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jerin sunayen 'yan majalisar jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta samu cewa cikin kadarorin da za'a kwace akwa wasu da yawa da suka hada da filin da ya kai eka 22 da shagunan zamani da wasu gidaje biyu dake da alaka da iyalan Marigayi Shehu Musa 'Yar'adua na gidauniyar sa.

Jami'in hulda da jama'ar na hukumar ICPC din Rasheedat A. Okoduwa tace sun kuduri aniyar daukar wannan matakin ne biyo bayan korafin da hukumar tattara haraji ta ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) ta kai masu.

A wani labarin kuma, A cigaba da cacar bakin da ake ta yi tsakanin jami'an rundunar sojin Najeriya da kuma hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) musamman ma a zaben gwamnan jihar Ribas, hukumar ta ce bata ce sojojin su je rumfar zabe ba.

Hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) ta yi wannan kalaman ne biyo bayan maganar da jam'iyyar APC ta yi akan cewa sojojin sun taimaka ne kawai wajen gudanar da zabuka masu sahihanci a jihar kamar yadda hukumar ta bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel