Yanzu Yanzu: Atiku, PDP sun shigar da korafi akan zaben Buhari

Yanzu Yanzu: Atiku, PDP sun shigar da korafi akan zaben Buhari

- A yanzu haka jam’iyyar PDP na cike korafinta akan kaddamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka yi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa na 2019

- PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, sun tattara wata tawagar lauyoyi a kotun roko wanda a yanzu haka suna aiki akan bin tsarin cike korafin

Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cike korafinta akan kaddamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka yi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa na 2019.

Jam’iyyar da dan takararta, Atiku Abubakar, sun tattara wata tawagar lauyoyi a kotun roko, bagiren kotun sauraron korafi akan zaben Shugaban kasa wanda a yanzu haka suna aiki akan bin tsarin cike korafin.

Yanzu Yanzu: Atiku, PDP sun shigar da korafi akan zaben Buhari
Yanzu Yanzu: Atiku, PDP sun shigar da korafi akan zaben Buhari
Asali: UGC

Mista Abubakar ya dade da kin amincewa da sakamakon zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, inda yayi zargin cewa anyi magudi. Ya sha alwashin kai saka,makon zaben gaban kotu.

Da farko kotu ta amince da rokon PDP na a bata dammar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben. Sai dai kotun ta dakile yunkurin jam’iyyar na bincikar kayayyakin.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: Ya kamata hukumomin tsaro su zama cikin shiri sosai – Dattawan Kano

A ranar Litinin lauyan Atiku mai jagora, Chris Uche ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Tims cewa an cike ka’idojin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel