Da dumin sa: Sanata Akpabio ya garzaya kotu kan faduwa zaben sa

Da dumin sa: Sanata Akpabio ya garzaya kotu kan faduwa zaben sa

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Najeriya kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress APC dake wakiltar mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso yamma, Sanata Godswill Akpabio ya garzaya kotu kan rashin yadda da kayen da ya sha a zaben da ya gabata.

Mai taimakawa Sanatan na musamman a harkokin yada labarai, Mista Anietie Ekong ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom inda kuma yace suna da yakinin samun nasara.

Da dumin sa: Sanata Akpabio ya garzaya kotu kan faduwa zaben sa
Da dumin sa: Sanata Akpabio ya garzaya kotu kan faduwa zaben sa
Asali: UGC

KU KARANTA: Zaben Ribas: Ana cacar baki tsakanin sojoji da INEC

Legit.ng Hausa a baya dai kafin zabe ta kawo maku cewa tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jaddada cewa jam'iyyar APC ce zatayi nasara a zabe mai zuwa a matakin tarayya da jihar Akwa Ibom saboda jam'iyyar PDP ta dade da mutuwa a jihar inda su kuma suka binne ta.

Sanata Akpabio ya sanar da hakan ne a yakin neman zaben a Abak, inda ya tabbatar da cewa sakamakon zabe zai yiwa gwamna Udom Emmanuel da mukarraban shi warwas, wanda yace zai nemi hanya mafi sauki don gujewa kaye.

Tsohon gwamnan ya zargi PDP da hayar bata gari don magudin zabe, amma kuma hakan ba zai tsorata APC ba saboda tuni ta fara murnar nasarar zabukan da za'ayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel