Kawai a ba duk wanda ya lashe zaben Kano - Tofa

Kawai a ba duk wanda ya lashe zaben Kano - Tofa

Shahararren dan siyasar nan na Najeriya, Bashir Othman Tofa ya yi kira ga 'yan takarar zaben gwamna a jihar Kano da su yarda da kaddara tsakaninsu duk wanda ya fadi zabe.

Alhaji Bashir Tofa wanda wanda ya kasance shugaban wata kungiyar ci gaban Kano, ya nuna fargabar tashin hankali a Kano idan har aka nemi sauya sakamakon zaben da za a sake a wasu mazabu na jihar.

A hira da yayi da shafin BBC yace: "Yanzu hakkin INEC ne ta fitar da abin da yake shi ne halal wanda za a yadda da shi ko da an tafi kotu.”

Kawai a ba duk wanda ya lashe zaben Kano - Tofa
Kawai a ba duk wanda ya lashe zaben Kano - Tofa
Asali: UGC

Ya kuma yi kira ga 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasar Kano da su ja hankalin magoya bayansu domin ganin an gudanar da zaben lafiya.

A ranar Asabar 23 ga watan Maris ne hukumar INEC ta ce za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano bayan sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar Kano Concerned Citizens Initiative (KCCI) ta bukaci hukumomin tsaro da su zama cikin shiri daga yanzu har zuwa kaddamar daakamakon zaben da za a sake a jihar.

KU KARANTA KUMA: INEC za ta yanke hukunci kan Okorocha kwanan nan

Shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa tare da sauran mambobin kungiyar sun yi wannan kiran yayinda suke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 18 ga watan Maris a Kano.

Tofa ya bayyana cewa kungiyar KCCI ta jajirce wajen tabbatar da cewar an magance duk wani aiki da ka iya tayar da rikicin siyasa, kafin, lokaci da kuma bayan zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel