INEC za ta yanke hukunci kan Okorocha kwanan nan

INEC za ta yanke hukunci kan Okorocha kwanan nan

Hukumar zabe mai zaman kanta a ranar Litinin, 18 ga watan Maris tace za ta yanke hukunci kan mataki na gaba da za ta dauka akan rigimar da ke tattare da kujerar sanata na yankin Imo ta yamma.

Rotimi Oyekanmi, babban sakataren hukumar zabe mai zaman kanta, ya fada ma jaridar The Guardian cewa hukumar ba ta bayar da takardar shaidar cin zabe ba ga kowani dan takara amma “za ta yanke hukunci kan abu na gaba da za ta yi.”

Wadanda suka shiga zaben kujerar sanata da aka gudanar tare da na Shugaban kasa a ranar 23 ga watan Fabarairu sun kasance yan takara 37 ciki harda gwmnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

INEC za ta yanke hukunci kan Okorocha kwanan nan
INEC za ta yanke hukunci kan Okorocha kwanan nan
Asali: UGC

Baturen zabe, Farfesa Ibeawuchi Innocent ya kaddamar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben. Ya samu kuri’u 97,762 inda ya doke babban abokin adawarsa Jones Onyereri na PDP wanda ya samu kuri’u 63,117.

Sai dai Innocent ya bayyana cewa shi ya kaddamar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben sakamakon barazana da ya fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka zuwa APC

Sai dai gwamnan ya soki zargin sannan ya zargi baturen zaben da shirya makirci.

Don haka ba a sanya sunan Okorocha ba cikin jerin wadanda aka baiwa takardar shaidar cin zabe sannan duk da zanga-zangar da yayi akan hukuncin, ba a bashi ba a lokacin da sauran zababbun sanatocin suka karbi nasu a makon da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel