Sake zabe: Ya kamata hukumomin tsaro su zama cikin shiri sosai – Dattawan Kano

Sake zabe: Ya kamata hukumomin tsaro su zama cikin shiri sosai – Dattawan Kano

Kungiyar Kano Concerned Citizens Initiative (KCCI) ta bukaci hukumomin tsaro das u zama cikin shiri daga yanzu har zuwa kaddamar daakamakon zaben da za a sake a jihar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa tare da sauran mambobin kungiyar sun yi wannan kiran yayinda suke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 18 ga watan Maris a Kano.

Tofa ya bayyana cewa kungiyar KCCI ta jajirce wajen tabbatar da cewar an magance duk wani aiki da ka iya tayar da rikicin siyasa, kafin, lokaci da kuma bayan zabe.

Sake zabe: Ba za a lamunci duk wani aiki na rikici ba – Dattawan Kano
Sake zabe: Ba za a lamunci duk wani aiki na rikici ba – Dattawan Kano
Asali: Facebook

Yace dattawan za su yi duk abunda ya kamata domin kare jihar, inda ya kara da cewa ba za su bari yankin ya kona kudirin jihar ba.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki yayinda yar ajin karshe a jami’a ta mutu a hatsarin mota a Sokoto (katin shaida)

Ya kuma bayyana cewa ya kamata a tura isassun tsaro ga dukkanin mazabu 234 a fadin kananan hukumomin.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Dakta Baffa Bichi, tsohon babban sakataren hukumar asusun manyan makarantun na kasa (TETFUND), ya kai ziyarar ban girma ga Abba Kabir Yusuf, dan tgakarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, domin nuna baya gare shi a bayyane.

A wani faifan bidiyo da Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamnan jihar Kano a bangaren sadarwar zamani, ya fitar a shafinsa na Tuwita a yau, Litinin, an ga Dakta Bichi tare da Abba sun cikin farinciki da walwala sun a gaisawa da jama’a kafin daga bisani su shiga wani daki.

Yakasai ya bayyana cewar Dakta Bichi ya ziyarci Abba ne domin nuna goyon baya gare shi a bayyane, a kokarinsa na daukar fansa a kan Ganduje da jam’iyyar APC saboda an cire shi daga mukaminsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel