Ni a karan kai-na, na fi Shugaban kasa Buhari arziki – Yemi Osinbajo

Ni a karan kai-na, na fi Shugaban kasa Buhari arziki – Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ya fi Mai gidan sa watau Shugaba Muhammadu Buhari arziki. Farfesa Osinbajo yace ya taba fadawa shugaban kasar cewa ya fi sa kudi.

Yemi Osinbajo ya bada labarin abin da ya auku tsakanin sa da shugaban kasar a 2015 a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya cike takardun da ke dauke da jerin dukiya da duk kadarorin da ya mallaka a gida da wajen Najeriya.

Farfesa Osinbajo yace a wancan lokaci ya fadawa shugaban kasar cewa abin kunya ne ace yana mataimakin sa, kuma ya fi sa kudi. Shugaban kasar ya ke cewa da mataimakin sa babu aibu a hakan domin shi soja ne ba komai ba.

KU KARANTA: Mai ba Shugaban kasa Buhari yana yi wa Osinbajo taurin kai

Ni a karan kai-na, na fi Shugaban kasa Buhari arziki – Farfesa Yemi Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo yaceya fi Shugaba Buhari arziki
Asali: Facebook

Shi kuma mataimakin shugaban kasa watau Osinbajo, rikakken Lauya ne wanda Duniya ta ke ji da shi, don haka shugaba Buhari yake ganin babu wani abin kunya don Yemi Osinbajo ya kere masa wajen dukiya da manyan kadarori.

Haka kuma mataimakin shugaban kasar yace a ganin sa dukiyar shugaban kasar raguwa ma raguwa ta ke yi ba karuwa ba tun daga lokacin da ya hau kan karagar mulki a 2015. Shugaban kasa Buhari dai yayi ritaya daga gidan Soja ne tun a 1985.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel