Da zafinsa: Mun haramtawa INEC karbar sakamakon zaben Bauchi - Kotu

Da zafinsa: Mun haramtawa INEC karbar sakamakon zaben Bauchi - Kotu

Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC daga ci gaba da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi wanda ya gudana a ranar 9 ga watan Maris.

Hukuncin wanda kotun ta bayar ya zo ne bayan da gwamnan jihar Bauchi mai ci a yanzu, Mohammed Abubakar da jam'iyyar APC suka shigar da kara, wanda kuma hukuncin zai ci gaba har sai an war ware shari'ar tsakanin bangarorin biyu.

A cikin takardar korafin, APC da Abubakar sun roki kotun da ta bayar da umurni da zai hana hukumar INEC dawowa da karbar sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa wanda jhukumar ta soke a baya dangane da zaben kujerar gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shugaban kasa Buhari ya gana da Sanwo Olu, zababben gwamnan Legas

Da zafinsa: Mun haramtawa INEC karbar sakamakon zaben Bauchi - Kotu
Da zafinsa: Mun haramtawa INEC karbar sakamakon zaben Bauchi - Kotu
Asali: UGC

Mai shari'a Ekwo a ranar Litinin a lokacin da ya ke karanta takarar korafin ya baiwa hukumar INEC umurnin gurfana gabanta a ranar Talata domin gabatar da dalilin da ta ke ganin bai dace kotun ta amince da bukatar masu shigar da kararba. Sai dai INEC, bisa wakilcin lauyanta, Tanimu Inuwa (SAN), a ranar Talata ya kalubalanci wannan korafi da aka shigar gaban kotun.

Mai shari'a Ekwo ya yanke hukuncin cewa tunda har karar an shigar da ita ne a rubuce kuma an sanar da INEC ta gurfana gaban kotun da hujjojinta a rubuce, wanda kuma ta gaba hakan, ya amince da bukatar bangaren masu karar.

A karashe, mai shari'ar ya umurci INEC da ta dakata daga ci gaba da karba, ko sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, har sai bangaren da ake kara ya gabatar da hujjoji da za su fi karfin na bangaren masu kara.

Da wannan mai shari'a Ekwo ya baiwa bangaren da ake kara damar gabatar da hujjojin kare kansu a ranar Laraba 20 ga watan Maris, inda za aci gaba da sauraron karar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel