Da duminsa: Shugaban kasa Buhari ya gana da Sanwo Olu, zababben gwamnan Legas

Da duminsa: Shugaban kasa Buhari ya gana da Sanwo Olu, zababben gwamnan Legas

Bisa rahotannin da muka samu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da zababben gwamnan jihar Legas, Jide Sanwo Olu tare da zababben mataimakin gwamnan jihar, Femi Hamzat, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Legit.ng Hausa ta tattara rahoto kan cewa shugaban kasar ya gana da zababben gwamnan da mataimakinsa a cikin ofishinsa a ranar Litinin, 18 ga watan Maris, kusan makwanni ukku da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki, wanda ya baiwa Mr Olu nasarar lashe zaben jihar Legas karkashin jam'iyyar APC.

KARANTA WANNAN: Kaduna: Yadda jarirai 6,000 za su kamu da cutar kanjamau a 2019 - UNICEF

Babajide Sanwo Olu ya samu kuri'u 739,445, wanda ya bashi damar lallasa abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Jimi Agbaje, wanda ya samu kuri'u 206,141, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.

Duba hotunan ziyarar da zababben gwamnan jihar Legas da shugaban kasa:

Da duminsa: Shugaban kasa Buhari ya gana da Sanwo Olu, zababben gwamnan Legas
Da duminsa: Shugaban kasa Buhari ya gana da Sanwo Olu, zababben gwamnan Legas
Asali: Twitter

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel