Gwamnati za ta kama duk iyayen da basu saka yayansu a makaranta ba

Gwamnati za ta kama duk iyayen da basu saka yayansu a makaranta ba

Gwamnatin tarayya zata fara gurfanar da duk uban daya ki sanya yayansa a makarantar boko matukar yaran sun kai shekarun shekarun shiga makaranta, kamar yadda Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Adamu ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 18 ga watan Maris yayin da yake ganawa da manema labaru a karshen makon data gabata, inda yace nan bada jimawa zai zama babban laifi idan iyaye suka ki sanya yayansu a makaranta.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Yadda wasu gagararrun yan fashi da makami suka fada komar Yansanda

“Idan ba mun fara kama iyayen dake kin sanya yayansu a makaranta tare da dauresu ba, ba zamu saukin adadin yaran dake zaune a gida suna yawo a kwararo kwararo lungu lungu a kasar nan ba. Akwai wasu da dama da har yanzu suke fakewa da addini da kabilanci.

“Don haka nan bada jimawa ba zamu fara aiki da dokar da zata haramta ma iyaye zaunar da yayansu a gida ba tare da sun sanyasu makaranta ba, tare da dauresu a kurkuku.” Inji shi.

Bugu da kari ministan ya bayyana cewa gwamnatin Buhari kashe naira biliyan 350 a harkar ilimi a Najeriya, yayin da gwamnatin data gabata ta kashe naira biliyan 360 daga 2009 zuwa 2014 a wajen sayan littafai, horas da Malamai, gine gine azuzuwa da sauransu.

Daga karshe ministan ya danganta cin hanci da rashawa da kuma burin siyasa da tasa gwamnatocin jahohi suka yi sake har sha’anin ilimi a matakin farko ya tabarbare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel