Hukumar ‘yan sanda ta yi karin bayani a kan tantance ma su neman aiki

Hukumar ‘yan sanda ta yi karin bayani a kan tantance ma su neman aiki

- Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewar ba ta fara tantance ma su neman aiki na shekarar 2019 ba

- Hukumar kula da rundunar ‘yan sanda (PSC) ta sanar da cewar a kalla mutane 315,032 suka nuna sha’awara aiki da rundunar ‘yan sanda bayan fitar da sanarwar daukan Karin ma’aikata 10,000

- PSC ta bayyana cewar ta yi mamakin yadda masu neman aikin suka mamaye ofishin ru dunar ‘yan sanda na jihohi domin tantance wa

Hukumar kula da rundunar ‘yan sanda (PSC) ta ce ba ta fara tantance masu sha’awar aiki da rundunar ‘yan sanda na shekarar 2019 ba.

Kimanin mutane 315,032 ne suka nuna sha’awar nuna sha’awar aiki da rundunar ‘yan sanda tun bayan fitar da sanarwar daukan Karin ma’aikata 10,000 a ranar 11 ga watan Janairu.

A kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kara daukan kananan ‘yan sanda domin bunkasa harkar tsaro a kasa.

Hukumar ‘yan sanda ta yi karin bayani a kan tantance ma su neman aiki
Hukumar ‘yan sanda ta yi karin bayani a kan tantance ma su neman aiki
Asali: UGC

A wani jawabi da ta fitar a yau, Litinin, 18 ga watan Maris, ta bakin Ikechukwu Ani, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, PSC ta bayyana cewar ba ta gayyaci masu neman aiki domin a fara tantance su ba.

DUBA WANNAN: Badakalar N544m: EFCC ta yiwa tuhumar Babachir kwaskwarima

Ya kara da cewa PSC ta yi mamakin yadda wasu daga cikin masu neman aikin suka mamaye ofishin rundunar ‘yan sanda na jihohi domin a tantance su.

Kwanan nan PSC zata sanar da masu sha’awar aiki da rundunar ‘yan sanda ranar da za a fara tantance su. Muna kira ga masu neman aiki da su yi watsi da duk wata sanarwa matukar ba daga PSC ta fito ba,” a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel