Yanzu Yanzu: Wani ginin ya sake ruftowa a Lagas (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Wani ginin ya sake ruftowa a Lagas (bidiyo)

Wani gini ya sake ruftawa a Lagas kasa da mako guda bayan irin hakan ya faru wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu yaran makaranta.

A cewar wani rahoto daga Sahara Reporters, ginin ya rufta ne a 57, Egerton Square, Oke Arin, Lagos Island.

Lamarin ya afku ne a ranar Litinin, 18 ga watan Maris.

An rahoto cewa tun da fari an sanya ginin cikin wadanda za a rushe.

Ana zargin mutane da dama sun mutu yayinda wasu suka lakea rushashen ginin. An tattaro cewa an ceto mutum hudu daga rusasshen ginin.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki yayinda yar ajin karshe a jami’a ta mutu a hatsarin mota a Sokoto (katin shaida)

Daraktan sashin kasha gobara na jihar Lagas, Rasaki Musbau yace ginin ya soma ruftawa ne, inda ya kara da cewa ma’aikatan kasha gobara sun kai mutane hudu da aka ceto asibiti.

A cewar Musbau dukkanin mutanen da aka ceto mazauna gidan ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel