Badakalar N544m: EFCC ta yiwa tuhumar Babachir kwaskwarima

Badakalar N544m: EFCC ta yiwa tuhumar Babachir kwaskwarima

A yau, Litinin, ne wata babbar gwamnatin tarayya dake zamanta a Maitama, Abuja, ta bawa huumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki damar yin kwaskwarima a kan tuhumar badakalar N544m da take yiwa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, tare da wasu mutane uku.

An fara gurfanar da Babachir a gaban kotu ranar 12 ga watan Fabrairu tare da Sulaiman Abubakar; darekta a kamfaninsa, da Apeh Monday; manajin darektan kamfanin sa da kuma wani ma’aikacin guda daya.

Alkalin kotun, Jastis Jude Okeke, ya amince da yin kwaskwarima ga tuhumar da ake yiwa Babachir bayan lauyan EFCC, Mista Ufom Uket, ya mika bukatar neman kara sunan kamfanin Josmon Technologies cikin tuhuma ta 6, 9 da 10.

Jastis Okeke ya bawa EFCC damar yin kwaskwarimar ne bisa dogaro da sashe 218 na ACJA.

Badakalar N544m: EFCC ta yiwa tuhumar Babachir kwaskwarima
Shugaban hukumar EFCC; Ibrahim Magu
Asali: Depositphotos

Kazalika, Jastis Okeke ya amince da bukatar lauyan dake kare wadanda ake tuhuma na barinsu su cigaba da cin moriyar belinsu da aka bayar tun a farko.

Jastis Okeke ya daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Afrilu domin fara sauraron hujjar kowanne bangare.

DUBA WANNAN: Abba Kyari ya bayyana abinda ya ke ci ma sa tuwo a aikin dan sanda

EFCC ta gurfanar da Babachir tare da ragowar mutanen uku bisa tuhumar su da aikata laifuka 10 dake da nasaba da hadin baki domin bayar da kwangila ga wasu kamfanoni mallakar Babachir ba tare da bin ka’ida ba.

EFCC na zargin Babachir da bawa kamfanoninsa kwangila ta miliyan N544,119,925.36 ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta EFCC ta zargi Babachir da bayar da kwangilar a karkashin wani shirin cire ciyawa da tsaftace sanasanin ‘yan gudun hijira da ofishin shugaban kasa ya dauki nauyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel