Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka zuwa APC

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka zuwa APC

- Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mista Peter Mbucho (ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Rt.Hon. Ibrahim Balarabe-Abdullahi, kakakin majalis jihar ya bayyana hakan a ranar Litinin yayinda yake karanta wasikar sauyin shekan Mbucho zuwa majalisa

- Mbucho ya bayyana cewa ya koma APC ne domin kawo wa mazabarsa tarin ci gaba

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mista Peter Mbucho (PDP-Akwanga ta arewa) a ranar Litinin, 18 ga watan Maris ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Rt.Hon. Ibrahim Balarabe-Abdullahi, kakakin majalis jihar ya bayyana hakan a ranar Litinin yayinda yake karanta wasikar sauyin shekan Mbucho a lokacin zaman majalisar a Lafia.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka zuwa APC
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka zuwa APC
Asali: UGC

Kakakin majalisar ya taya Mbucho murnar dawowa jirgin mataki na gaba.

Da yake jawabi, Mbucho ya bayyana cewa ya koma APC ne domin kawo wa mazabarsa tarin ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki yayinda yar ajin karshe a jami’a ta mutu a hatsarin mota a Sokoto (katin shaida)

Tsohon Shugaban marasa rinjayen ya bayyana cewa zai ci gaba da amfani da tarin kwarewarsa wajen kawo ci gaba ga gwamnatin APC a dukkan matakai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel