Ya zama wajibi INEC ta sanar da 'yan Nigeria gaskiya kan zaben jihar Bauchi - APC

Ya zama wajibi INEC ta sanar da 'yan Nigeria gaskiya kan zaben jihar Bauchi - APC

- Wani jigo a APC, Yekini Nabena ya ce INEC na da amsoshi da dama da ya kamata ta amsa dangane da zaben gwamnan jihar Bauchi

- Nabena ya bukaci jam'iyyar PDP da ta manta da wani mafarkin da ta ke yi na lashe zaben gwamnan jihar Bauchi

- Nabena ya ce idan har ba wai don shirin tafka magudi ba, ta ya za ayi APC ta lashe kujeru 21 a majaisar wakilan tarayya yayin da PDP ta ke da kujeru 5 amma a ce PDP ta yi nasara?

Wani jigo a APC, Yekini Nabena ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na da amsoshi da dama da ya kamata ta amsa dangane da zaben gwamnan jihar Bauchi da kuma sabon matakin da ta dauka na ci gaba da karbar sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke a jihar.

Nabena ya bukaci jam'iyyar PDP da ta manta da wani mafarkin da ta ke yi na lashe zaben gwamnan jihar Bauchi, yana mai cewa babu wani sihiri da zai iya baiwa PDP a jihar bauchi nasara duba da cewa ta fadi warwas a kowanne bangare.

Ya kalubalanci hukuncin INEC na bayyana dan takarar jam'iyyar PRP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Katagum a majalisar wakilan tarayya, yana mai cewa "ya kamata a bayyana zaben mazabar a matsayin zaben da bai kammala ba saboda kuri'un da aka soke, 5,211 sun zarce banbancin kuri'un manyan jam'iyyun biyu, 4,704."

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Jonathan ya kira Gbenga Daniel, ya roke shi da ya tsaya a PDP

Ya zama wajibi INEC ta sanar da 'yan Nigeria gaskiya kan zaben jihar Bauchi - APC
Ya zama wajibi INEC ta sanar da 'yan Nigeria gaskiya kan zaben jihar Bauchi - APC
Asali: Twitter

Nabena wanda kuma shine mataimakin sakataren APC na kasa ya ce idan har ba wai don shirin da aka yi na tafka magudin zabe domin ganin an tunkude gwamna Mohammed Abubakar ba, ta ya za ayi APC ta lashe kujeru 21 a majaisar wakilan tarayya yayin da PDP ta ke da kujeru 5 amma a ce PDP ta zama a gaba?

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, Nabena ya ce rahotannin gaza yin amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a a karamar hukumar Bauchi "wani babban lamari ne da bai kamatgga hukumar zabe ta kyale haka nan ba. Jam'iyyar PDP ta riga da ta san cewa za ta sha kasa idan har aka sake gudanar da wani zaben zagaye na biyu."

Ya jaddada cewa akwai bukatar sake gudanar da zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, yana mai cewa malamar zaben karamar hukumar, Mrs Dominion Anosike, ta shaidawa duniya yadda aka ci mutuncinta yayin da ta ke tattara sakamakon zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel