Tushen arziki: Yanzu Nigeria na fitar da tan 8m na shinkafa kowacce shekara - RIFAN

Tushen arziki: Yanzu Nigeria na fitar da tan 8m na shinkafa kowacce shekara - RIFAN

- Kungiyar manoman shinkafa ta kasa RIFAN ta ce a yanzu Nigeria na samar da kalla tan miliyan takwas na shinkafa a kowacce shekara

- Legit.ng Hausa ta tattara rahoton cewa kungiyar ta ce Nigeria a yanzu ba ta da wani zabi da ya wuce haramta shigo da shinkafa kasar gaba daya kafin karshen 2019

- Da wannan kungiyar ta ce kasar ita ce mafi girma da wajen samar da shinkafa a kasashen Afrika

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa RIFAN ta ce a yanzu Nigeria na samar da kalla tan miliyan takwas na shinkafa a kowacce shekara, tana mai karawa da cewa kasar ita ce mafi girma da wajen samar da shinkafa a kasashen Afrika.

Shugaban kungiyar, Aminu Goronyo ne ya bayyana hakan, wanda kuma ya ce Nigeria na da lokacin yin noma guda biyu a kowacce shekara, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaitoshi yana cewa.

Legit.ng Hausa ta tattara rahoton cewa Goronyo, wanda ya ce Nigeria a yanzu ba ta da wani zabi da ya wuce ta kakaba dokar haramta shigo da shinkada kasar gaba daya kafin karshen 2019, ta bayyana cewa akalla ana noma tan miliyan 4 a kowacce kakar noma.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: APC ta kori Airhiavbere daga jam'iyyar

Tushen arziki: Yanzu Nigeria na fitar da tan 8m na shinkafa kowacce shekara - RIFAN
Tushen arziki: Yanzu Nigeria na fitar da tan 8m na shinkafa kowacce shekara - RIFAN
Asali: Depositphotos

Ya ce: "Muna da lokutan noma guda biyu, kuma a kowanne okaci ana samar da akalla tan miliyan 4 na shinkafa, wanda zai bamu tan miliyan 8 a kowacce shekara."

Goronyo ya ce akwai hadin guiwa tsakanin kungiyar da gwamnatin taayya wanda ke da nufin rage yawan kudaden da ake kashewa na noman shinkafar a kasar.

A cewarsa, hadakar za ta kuma taimaka wajen rage farashin shinkafa a kasuwannin kasar.

Ya ce: "Muna da isassun kayan aiki a kasa, muna da masu samar da shinkafa masu yawa a kasar, wanda ke nufin cewa akwai bukatar rage farashin kudin shinkafar a nan gaba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel