Yanzunnan: An sauya kiyasin takardun kadarori na ne a ofishin CCT – Onnoghen ga kotu

Yanzunnan: An sauya kiyasin takardun kadarori na ne a ofishin CCT – Onnoghen ga kotu

- Dakataccen Shugaban alkalan Najeriya, Justis Walter Onnoghen ya fada ma kotun kula da da’ar ma’aikata cewa an sauya fam din kaddamar da kadarorinsa da ke a gaban ta

- Ya bayyana hakan ne bayan kotun ta gabatar da fam din kaddamar da kadarorin nasa a matsayin hujja

Dakataccen Shugaban alkalan Najeriya, Justis Walter Onnoghen ya fada ma kotun kula da da’ar ma’aikata cewa an sauya fam din kaddamar da kadarorinsa da ke a gaban kotun.

Ya lura da hakan ne bayan kotun ta gabatar da fam din kaddamar da kadarorin nasa a matsayin hujja.

Gwamnatin tarayya ta bude shari’a ne a ranar Litinin, 18 ga watan Maris. An dawo da Onnoghen don ci gaba da shari’a bayan hutun sa’o’i 72.

Yanzunnan: An sauya kiyasin takardun kadarori na ne a ofishin CCT – Onnoghen ga kotu
Yanzunnan: An sauya kiyasin takardun kadarori na ne a ofishin CCT – Onnoghen ga kotu
Asali: Twitter

Wani rahoton likita da lauyansa, Cif Adegboyega Awomolo (SAN), ya gabatar a gaban kotun a zama na karshe da suka yi ya nuna cewaa Onnoghen na fada da ciwon hakori da kuma hawan jini sannan likitansa ya ba da shawarar kwantar dashi na sa’o’i 72.

Da farko dai kotun karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Umar ta dage zama zuwa ranar Litinin (yau) domin ci gaba da shari’an.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari

Lokacin da lamarin ya taso, gwamnatin tarayya tau de shari’arta ta hanyar kiran shaidan farko, Mista James Akpala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel