Babbar magana: APC ta kori Airhiavbere daga jam'iyyar

Babbar magana: APC ta kori Airhiavbere daga jam'iyyar

- Jam'iyyar APC a gundumar ta 1 da ke karamar hukumar Oredo, ta kori Janar Charles Airhiavbere daga jam'iyyar bisa zarginsa da cin amanar jam'iyya

- An dakatar da Janar Airhiavbere wanda shi ne dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC a 2016, a wani taron shuwagabannin jam'iyyar

- Haka zalika APC ta zarge shi da hadin baki da PDP, a lokacin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya

Jam'iyyar APC a gundumar ta 1 da ke karamar hukumar Oredo, ta kori Janar Charles Airhiavbere daga jam'iyyar bisa zarginsa da cin amanar jam'iyya a yayin da aka gudanar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

An dakatar da Janar Airhiavbere wanda shi ne dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC a 2016, a wani taron shuwagabannin jam'iyyar inda aka saurari rahoton wani kwamitin bincike da aka kafa domin bin diddigi tare da gano gaskiyar zargin da ake yi masa.

Daga cikin zargin da ake yiwa Janar Airhiavbere sun hada da cewa ya rike shaidar makalawa a wuya da ke nuni da zama jami'in jam'iyya da kuma wasu kayayyaki mallakan APC wanda ya kawo tsaiko a ayyukan jami'an jam'iyyar a wajen zaben.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kotu ta kori tsagin APC da Ogboru ya yi takarar gwamnan Delta

Babbar magana: APC ta kori Airhiavbere daga jam'iyyar
Babbar magana: APC ta kori Airhiavbere daga jam'iyyar
Asali: UGC

Haka zalika APC ta zarge shi da hadin baki da PDP.

A cewar wata sanarwa daga shuwagabannin jam'iyyar APC na gunduma ta 1, "La'akari da cin amanar jam'iyya da Janar Airhiavbere ya yi, da kuma yiwa APC zagon kasa, mu shuwagabannin jam'iyyar Orede gunduma ta 1, mun karaya da Janar Airhiavbere.

"Da wannan ne kuma muka sanar da dakatar da shi daga jam'iyyar kwata-kwata."

Sai dai da ya ke martani kan wannan kora da aka yi masa, Janar Airhiavbere ya ce an shirya hukuncin korar ne domin dakatar da shi daga tsayawa takarar gwamnan jihar karkashin APC domin karawa da gwamna Obaseki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel