Da duminsa: Kotu ta kori tsagin APC da Ogboru ya yi takarar gwamnan Delta

Da duminsa: Kotu ta kori tsagin APC da Ogboru ya yi takarar gwamnan Delta

Rahoton da muka samu yanzu na nuni da cewa wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta kori tsagin jam'iyyar APC da ke karkashin shugabancin Jones Erue a jihar.

Kotun ta yanke wannan hukuncin kasa da awa daya a garin Asaba.

Tsagin jam'iyyar APC da ke karkashin Erue, sun gabatar da Great Obgboru, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Delta a zaben 2019 da aka kammala a makwannin baya.

KARANTA WANNAN: Ilimi: Kurkukun Ikoyi ta dauki nauyin bursononi 24 domin zana jarabawar JAMB

Cikakken labarin yana zuwa...

Da duminsa: Kotu ta kori tsagin APC da Ogboru ya yi takarar gwamnan Delta
Da duminsa: Kotu ta kori tsagin APC da Ogboru ya yi takarar gwamnan Delta
Asali: UGC

A wani ci gaban kuwa; Kwanturolan hukumar kula da gidajen yari ta kasa reshen jihar Legas, Tunde Ladipo, ya ce akalla bursunoni 24 ne daga gidan kurkukun Ikoyi za su zana jarabawar share fage shiga manyan makarantu UTME zangon shekarar 2019.

Ladipo ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris a Legas.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta sanya ranar 1 ga watan Afrelu a matsayin ranar da za ta gudanar da jarabar 'mock' wacce ba tilas ba ce ga dalibai, sannan ta sanya ranar 11 ga watan Afrelu a matsayin ranar fara UTME a fadin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel