Banbarakwai: Alkalin Alkalai, Walter Onnoghen da aka dakatar ya bayyana a gaban kotu

Banbarakwai: Alkalin Alkalai, Walter Onnoghen da aka dakatar ya bayyana a gaban kotu

Tawagar Alkalan da ke tuhumar Alkalin Alkalai na kasa da aka dakatar, Walter Onnoghen sun gabatar da shaidansu na farko a gaban kotun da'ar ma'aikata CCT a yau.

An dai dakatar da sauraron shari'ar ne tun ranar 12 ga watan Maris na wannan shekarar sakamakon rashin lafiya da aka ce CJN Onnoghern yana fama da ita kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Onnoghen ya bayyana a kotun da'ar ma'aikatan cikin yanayi mai kyawu misalin karfe 10 na safiyar yau da aka fara sauraron shari'ar.

Banbarakwai: Alkalin Alkalai da aka dakatar ya bayyana a gaban kotu
Banbarakwai: Alkalin Alkalai da aka dakatar ya bayyana a gaban kotu
Asali: Depositphotos

Jagoran lauyoyin da ke tuhumar Onnoghen, Aliyu Umar (SAN) ya sanar da lkotun cewar shedansa a shirye ya ke jim kadan kuma sai ya gabatar da shaidansa na farko a gaban kotun bayan an bashi izinin aikata hakan.

An gayyaci shaidan na farko, babban jami'in bincike na Cibiyar Da'ar Ma'aikata CCB, James Opola ya shiga akwatin bayar da sheda domin ya fadawa kotun dukkan abinda ya sani a game da shari'ar.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel