Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari

Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari

Gwamna Mohammed Abdullahi na jihar Bauchi a ranar Litinin, 1 ga watan Maris ya ziyarci fadar Shugaban kasa kasa da sa’oí 24 bayan fadar Shugaban kasa ta nisanta Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga ayyukan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Kkamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa gwamnan ya gana da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajon a makon da ya gabata inda yaki cewa komai game da ganawar tasu.

Da yake Magana da manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan ganawar sirrin da suka yi Shugaban kasar, gwamnan ya bayyana cewa ya sanar da Shugaban kasar akan halin da siyasar jihar Bauchi ke ciki a yanzu.

Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari
Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

Yayi bayanin cewa matsayar INEC game da sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi na iya haifar da matsala.

Sai da, fadar Shugaban kasa a wata sanarwa da ta fitar ta hannun Garba Shehu a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris yace Shugaban kasar ya dauki alkawarin kin sanya baki a zaben da za a sake gudanarwa a wasu jihohi, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin adalci da abun dariya sukar da ake yiwa Buhari na kin sanya baki a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnati ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas

A ranar Juma’a ne hukumar zabe mai zaman kanta ta yan shawarar ci gaba da kirga kuri’un zaben gwamna na jihar Bauchi sannan tana iya kaddamar da wanda ya lashe zaben wanda aka bayyana a matsayin ba kammalalle ba tare da wasu jihohi biyar a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel