Ba za mu ba Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabe ba – INEC

Ba za mu ba Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabe ba – INEC

Mun samu labari Hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta hakikance a kan cewa ba za ta bada takardar da ke nuna shaidar lashe zabe ga Mai girma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ba.

Hukumar zabe na INEC tace sam ba za ta bada satifiket din nasara ga Rochas Okorocha wanda yayi takarar Sanata a jihar Imo ba. Babban Kwamishinan INEC na yada labarai, Festus Okoye ya bayyana wannan dazu da safe.

Festus Okoye yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jaridar Channels TV a yau Litinin. Hakan na zuwa ne bayan an sanar da cewa Rochas Okorocha ne ya lashe zaben Sanatan Imo ta Yamma da aka yi kwanaki.

KU KARANTA: APC ta na so Ahmad Lawan ya rike Majalisar Dattawa Najeriya

Ba za mu ba Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabe ba – INEC
INEC ta hana Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha satifiket
Asali: Depositphotos

Barista Okoye yace Baturiyar zaben da tayi aiki a jihar Imo ta tabbatar da cewa an tursasa mata ne da ta sanar da Rochas Okorocha na APC a matsayin wanda ya ci zaben Sanata. Wannan ya sa dole tace jam’iyyar APC ce ta zo ta farko.

Gwamnan mai shirin barin-gado yayi kokarin nuna cewa ya ci zaben sa hankali kwance ba tare da nunawa jami’an INEC karfi ba. Sai dai duk da haka INEC ba ta gwamnan satifiket kwanaki lokacin da ta rabawa wadanda su ka ci zabe ba.

Festus Okoye yace ba za su ba duk wani wanda ya ci zabe ta hanyar tursasawa jami’an INEC su rubuta sakamakon da su ke so ba. INEC tayi gargadi cewa ba za ta yarda da magudi bam sannan tace dole ‘yan siyasa su zama masu bin doka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel