Dubu ta cika: Yadda wasu gagararrun yan fashi da makami suka fada komar Yansanda

Dubu ta cika: Yadda wasu gagararrun yan fashi da makami suka fada komar Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da kama wasu gagga gaggan yan fashi da makami guda biyu da suka yi kaurin suna wajen addaba tare da takura ma al’umma mazauna yankin Lekki na jahar Legas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito DPO na Yansandan Maroko, CSP Isah Abdulmajid ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, inda yace sun kama yan fashin da suka hada da Adebayo Ayomide da Isaac David jim kadan bayan sun yi ma wasu mata fashin wayoyinsu guda biyu.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta tura ma Buhari sabon babban dogari

Kaakakin Yansandan Maroko, DSP Bala Elkana ya bayyana cewa da misalin karfe 9 na daren Asabar, 9 ga watan Maris suka samu nasarar kama yan fashin, a daidai lokacin da DPO da yaransa suke aikin sintiri a tsakanin Lekki da Ikoyi.

“Ana cikin sintiri sai muka tarar da wasu yan mata biyu Gbemi da Hannah cikin halin firgici da razana a daidai gadar Lekki-Ikoyi, da muka tambayesu sai suka fada mana cewa yanzu wasu yan fashi suka nuna musu bindiga suka kwace wayoyinsu.

“Nan da nan muka rankaya zuwa hanyar da yan fashin suka bi kamar yadda matan suka nuna mana, mukayi sa’an cimmusu, inda muka cajesu, anan muka gano wayoyin yan matan, bindiga guda daya, da kuma adda, mun kwace kayan duka, sa’annan muka garkamesu a caji ofis.” Inji shi.

Daga karshe Elkana yace yan fashin sun amsa laifinsu, kuma tuni kwamandan rundunar Yansanda dkae da yan fashi da makami, SARS, Zubairu Muazu ya bukaci a turo masa yan fashin domin su cigaba da gudanar da bincike akansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel