Matashi ya aikata ma Magidanci aika aika ta kan ya hanashi sigari

Matashi ya aikata ma Magidanci aika aika ta kan ya hanashi sigari

Ke duniya ina zaki damu ne? wanann wani irin rayuwa muke ciki a yau, inda karami baya ganin girman babba, shi kuma babba baya tausaya ma karami, kuma baya rike girmansa. Irin wannan zama kara zubene ke janyo samun matsala a tsakanin al’umma.

Wannan shine kwatankwacin lamarin daya faru a jahar Legas, inda wani matashi dan shekara 23 Joachim Kikogble ya yi amfani da reza wajen yanka makwabcinsa saboda ya ki ya saya masa karan sigari.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta tura ma Buhari sabon babban dogari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar Yansandan jahar Legas tayi ram da Kikogble, kuma ta gurfanar dashi gaban wata kotun majistri dake unguwar Yaba na jahar Legas, inda take da tuhumarsa da cin zarafi, amma ya musanta laifin.

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Modupe Olaluwoye ya bayyana ma kotu cewa Kikogble yayi amfani da reza ne wajen yankan makwabcinsa Solomon Mifokpo kawai don ya ki sayen masa karansigari, dukkaninsu kuma mazauna Yaba ne.

A jawabinsa Dansandan, Kikogble ya aikata laifin ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Litinin, 11 ga watan Maris a titin Oko-Agban dake cikin unguwar Yaba, bayan ya nemi Solomon ya saya masa sigari.

“Ya mai sharia Kikogble ya tare Solomon yayin da yake tafiya a cikin layinsu ne inda ya nemi ya saya masa karan sigari, amma da Solomon yaki, sai cacar baki ya kaure a tsakaninsu, daga nan sai fada, ba tare da bata lokaci ba Kikogble ya ciro reza daga aljihunsa ya yanki Solomon, da kyar aka tsayar da jinin dake zuba a wani shagon shan magani.” Inji shi.

Sai dai biyo bayan musanta aikata laifin, Alkalin kotun, Mai sharia Oluwatoyin Oghere ta bada belinsa Kikogble akan kudi naira dubu hamsin, N50,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa akan dubu hamsin hamsin, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa 26 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel