Yanzu Yanzu: Gwamnati ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas

Yanzu Yanzu: Gwamnati ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas

Gwamnatin tarayya ta rufe shahararren cibiyar nan na kasuwan da ke Lagas wato ‘Trade Fair’. A yanzu haka yan kasuwan da basu san da lamarin ba sun isa shagunansu a cibiyar don gudanar da harkokinsu na yau da kullun abun mamaki sai kawai suka tarar anyiwa kofar shiga kasuwan kawanya.

Har yanzu yan kasuwa na cikin juyayi da kuma mamaki kan lamarin domin basu da masani akan kowani lamari da ya yi sanadiyar rufe harabar kasuwar ko kuma samun bayani kafin rufe wajen.

Wani mai amfani da shafin twitter, Chibuzor wanda da ya bayyana hakan yace dukkanin kungiyoyin kasuwar sun jinginar da harkokinsu a ranar Litinin, 18 ga watan Maris domin yin zanga-zanga akan rufe kasuwan.

Yanzu Yanzu: Gwamnati ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas
Yanzu Yanzu: Gwamnati ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Ban san an dakatar da Onnoghen ba kafin a rantsar da ni – Muhammad

“Dukkanin kungiyoyi a cibiyar kasuwancin sun jingine ayyuka yau domin yin zanga-zanga akan matakin kwace kasuwar ta karfin tuwo da gwamnatin jihar Lagas tayi.” Inji shi.

A wani lamari na daban, mun ji cewa rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da kama wasu gagga gaggan yan fashi da makami guda biyu da suka yi kaurin suna wajen addaba tare da takura ma al’umma mazauna yankin Lekki na jahar Legas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito DPO na Yansandan Maroko, CSP Isah Abdulmajid ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, inda yace sun kama yan fashin da suka hada da Adebayo Ayomide da Isaac David jim kadan bayan sun yi ma wasu mata fashin wayoyinsu guda biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel