INEC: Dalilin da yasa bamu bari Atiku ya duba kayayyakin zabe ba

INEC: Dalilin da yasa bamu bari Atiku ya duba kayayyakin zabe ba

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta fito ta yi bayani da abinda yasa ta hana dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, duba kayayyakin zabe.

Atiku ya garzaya kotu ne bayan fadi a zaben 23 ga watan Febrairu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari. Amma kakakin jam'iyyar PDP, ya saki jawabin cewa hukumar ta ki bin umurnin kotu kuma ta hana Atiku ganin kayayyakin.

Diraktan labaran hukumar, Oluwole Osaze-Uzzi, ya karyata maganar yayinda yake bayani ga manema labarai ranar Lahadi, yace:

" Ba gaskiya bane cewa an hana jam'iyyar PDP da dan takararta duba kayayyakin zabe. Wannan karya ne. A iyakan ilimina, bamu sau takardar bukatarsu ba sai ranar Juma'a. Kuma muna shirye da basu abinda suke so duk lokacin da suka shirya."

Mai magana da yawun shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanm, ya bayyanawa jaridar The Cable cewa hukumar zata bi umurnin koti muddin ta sami umurnin a rubuce.

Yace: "Kowa ya sani cewa tun lokacin da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, hukumar ta dukufa tana aiki kan abubuwan da suka shafi zaben majalisar dokokin tarayya, gwamnoni, majalisun dokokin jiha da kuma zaben birnin tarayya."

"Ranar Alhamis da ya gabata, hukumar ta gabatar da takardar shaidan nasara a zabe ga sabbin sanatoci da sabbin yan majalisar wakilai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel