Yanzu-yanzu: Hankalin jama'a ya tashi yayinda aka kashe kwamandan Soji a Bauchi

Yanzu-yanzu: Hankalin jama'a ya tashi yayinda aka kashe kwamandan Soji a Bauchi

Gidan Soja ta waye gari ranar Litnin, 18 ga watan Maris, 2019 cikin jimami sakamakon kisan Kwamandan 33 Atilari Birged, Kanal Mohammed, na hukumar Soja a barikin Shadawanka dake jihar Bauchi, Arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan kisan ya tayar da hankulan jama'ar garin saboda tsoron abinda zai biyo baya. Har yanzu dai ba'a tabbatar da wadanda sukayi kisan ba, shin yan fashi ne ko kuma makasa amma majiya ta bayyana cewa yan fashi ne.

Wannan abu da ya faru a hanyar Bauchi zuwa Jos ya faru ne ranar Lahadi yayinda marigayin ke tukin babur.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da basarake a jihar Edo

Wata majiya tace: "An harbi kwamandan 33 Atilari birged na barikin Shadawanka a jihar Bauchi, Kanal Mohammed Barack, har lahira. An harbesa ne ranar Lahadi a hanyar Jos yayinda yake tuka babur daga Kaduna. Dan jihar Kano ne."

A daidai lokacin da muke kawo wannan rahoto, an fara shirye-shiryen kai gawarsa Kano domin jana'iza bayan kammala al'adun gidan soja ga mamacinsu.

Yayinda aka tuntubi kakakin 33 Atilari birged, Manjo Yahaya Nasir Kabara, ya tabbatar da labarin inda ya gaskata.

Yayinda aka bukaci bayanin abinda ya faru yace abu ne mai bukatar bincike ; muna kan bincike. Zan tuntubeku idan muka gano wani abu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel