Ban san an dakatar da Onnoghen ba kafin a rantsar da ni – Muhammad

Ban san an dakatar da Onnoghen ba kafin a rantsar da ni – Muhammad

Justis Tanko Muhammad, mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya yace shi bai da masaniya akan kowani umurni da kotun kula da da’ar ma’aikata ta bayar akan Justis Walter Onnoghen, dakataccen Shugaban alkalan kasar.

Yace ya amince da rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban alkalai “domin ra’ayin kasar da kuma kundin tsarin mulki.”

Tako ya fadi hakan ne yayinda yake mayar da martini ga ayar tambaya da kungiyar alkalan kasar ta dasa a kansa, kan amincewa da yayi aka rantsar da shi a matsayin Shugaban alkalan kasar ba tare da amincewar majalisar ba.

Ban san an dakatar da Onnoghen ba kafin a rantsar da ni – Muhammad
Ban san an dakatar da Onnoghen ba kafin a rantsar da ni – Muhammad
Asali: Facebook

Wata kungiya mai suna Centre for Justice and Peace Initiative c eta dasa ayar tambayar sannan ta gabatar da takardar korafin ga majalisar alkalai inda ta bukaci cewa a tsigee Tanko a matsayin mukaddashin Shugaban alkalai.

Tanko ya kuma bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya bukatar amincewar majalisar alkalan kasar kafin ya rantsar da shi a matsayin mukkadashin Shugaban alkalan inda ya kara da cewa har yanzu Justis Walter Onnoghen ne Shugaban kungiyar domin dakatar da shi kawai aka yi.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya yayi kira ga a sa bam a masallacin Abuja bayan harin masallaci da aka kai New Zealand

Tanko ya kuma kara da cewa bai san an dakatar da Onnoghen be a lokacin da aka gayyace shi zuwa fadar Shugaban kasa don rantsar da shi a matsayin mukaddashin Shugaban alkalan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel