Kisan Kaduna: An tura rundunar hadin gwuiwa ta sojoji da 'yan sanda don kwantar da tarzoma

Kisan Kaduna: An tura rundunar hadin gwuiwa ta sojoji da 'yan sanda don kwantar da tarzoma

Gwamnatin tarayya ta hada tare da tura wata rundunar hadin gwuiwa ta kwararrun jami'an sojoji da 'yan sanda a kauyen Nandu Gbok dake a karamar hukumar Sanga, jihar Kaduna domin kwantar da tarzoma inda wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 9 da kona gidaje 30.

Rundunar hadin gwuiwar dai ta bayar da tabbacin samar da zaman lafiya tabbatacce a kauyen da ma sauran garuruwan jihar tare da kamo wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban alkali don fuskantar shari'a.

Kisan Kaduna: An tura rundunar hadin gwuiwa ta sojoji da 'yan sanda don kwantar da tarzoma
Kisan Kaduna: An tura rundunar hadin gwuiwa ta sojoji da 'yan sanda don kwantar da tarzoma
Asali: Facebook

KU KARANTA: Cacar baki tsakanin Sojoji da hukumar INEC

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun kawo maku labarin harin da aka kai kauyen na Nandu a ranar Asabar din da ta gabata wanda kuma kawo yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai harin.

Haka ma dai mun ruwaito maku cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ya jajantawa al'ummar jihar musamman ma iyalan wadanda harin 'yan binda ya shafa a kauyen Nandu dake a cikin karamar hukumar Sanga wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9 da yammacin yau.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin gwamnan na musamman a fannin yada labaru, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ya kuma wallafa a shafukan gwamnan dake dandalin sadarwar zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel