Ilimi: Kurkukun Ikoyi ta dauki nauyin bursononi 24 domin zana jarabawar JAMB

Ilimi: Kurkukun Ikoyi ta dauki nauyin bursononi 24 domin zana jarabawar JAMB

- Kwanturolan hukumar kula da gidajen yari ta kasa reshen jihar Legas, Tunde Ladipo, ya ce akalla bursunoni 24 ne za su zana jarabawar JAMB

- Ladipo ya ce tuni JAMB ta kammala dukkanin shirye shirye na tabbatar da cewa bursunonin sun zana jarabawar ba tare da matsala ba

- Kwanturolan hukumar ya ce ana sa ran bursunonin za su samu kyakkyawan sakamako a jarabawar

Kwanturolan hukumar kula da gidajen yari ta kasa reshen jihar Legas, Tunde Ladipo, ya ce akalla bursunoni 24 ne daga gidan kurkukun Ikoyi za su zana jarabawar share fage shiga manyan makarantu UTME zangon shekarar 2019.

Ladipo ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris a Legas.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta sanya ranar 1 ga watan Afrelu a matsayin ranar da za ta gudanar da jarabar 'mock' wacce ba tilas ba ce ga dalibai, sannan ta sanya ranar 11 ga watan Afrelu a matsayin ranar fara UTME a fadin kasar.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Hankalin jama'a ya tashi yayinda aka kashe kwamandan Soji a Bauchi

Ilimi: Kurkukun Ikoyi ta dauki nauyin bursononi 24 domin zana jarabawar JAMB
Ilimi: Kurkukun Ikoyi ta dauki nauyin bursononi 24 domin zana jarabawar JAMB
Asali: Twitter

A cewar Ladipo, hukumar zana jarabawar ta kammala dukkanin shirye shirye na gudanar da jarabawar ga bursunonin ba tare da samun matsala ba a muhallansu.

Ya yi nuni da cewa bursunonin wadanda suka samu kyakkyawan horo a makarantar da ke cikin gidan yarin, sun nuna kwazonsu da dagewarsu ta ganin sun samun gaggarumar nasara a jarabawar

Kwanturolan ya kara da cewa, idan har aka yi la'akari da ingancin makarantar da ke cikin gidan yarin, da kuma yadda ake horas da bursunonin yadda za su zana jarabawar ta hanyar na'ura mai kwakwalwa, to kuwa ba shakka za su samu sakamako mai kyau.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel