Zaben 2019: Cacar baki ta yi tsauri tsakanin sojoji da hukumar INEC

Zaben 2019: Cacar baki ta yi tsauri tsakanin sojoji da hukumar INEC

A cigaba da cacar bakin da ake ta yi tsakanin jami'an rundunar sojin Najeriya da kuma hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) musamman ma a zaben gwamnan jihar Ribas, hukumar ta ce bata ce sojojin su je rumfar zabe ba.

Hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) ta yi wannan kalaman ne biyo bayan maganar da jam'iyyar APC ta yi akan cewa sojojin sun taimaka ne kawai wajen gudanar da zabuka masu sahihanci a jihar kamar yadda hukumar ta bukata.

Zaben 2019: Cacar baki ta yi tsauri tsakanin sojoji da hukumar INEC
Zaben 2019: Cacar baki ta yi tsauri tsakanin sojoji da hukumar INEC
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Ba ruwan sojoji a zaben da aka yi - Mataimakin gwamnan Bayelsa

Sai dai hukumar ta bakin jami'in ta dake hulda da jama'a, Mista Festus Okoye ta bayyana cewa ita ba ta ce akai sojoji ba a rumfunan zaben kuma ma zata tattauna da shugabannin rundunar domin ganin sojojin sun tsaya inda ya kamata su tsaya a zabukan da za'a sake yi.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa hukumar zabe ta kasa watau INEC ta saka ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da zata gudanar da zagaye na biyu na zaben gwamnonin jahoji shida sakamakon rashin kammaluwar zaben da aka gudanar.

Jahohin da za'a sake zabukan sun hada da Kano, Sokoto, Filato, Benue da Adamawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel