Labaran karya ne ke haddasa rikicin zabe - Buratai

Labaran karya ne ke haddasa rikicin zabe - Buratai

Laftanal Janar Tukur Buratai, babban hafsan sojin Najeriya yace labaran karya ne ke haddasa yawan rike-riken zabe.

Da yake jawabi a jihar Bayelsa lokacin kaddamar da sabbin ayyuka a sansanin soji a ranar 16 ga watan Maris wanda aka sanya wa suna sansanin Buratai, Shugaban sojin yace yada labaran karya ne ke kai damokradiyya kabarinta cikin sauri da kuma ayyukan soji, jaridar Guardian ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Buratai wanda ya samu wakilcin kwamandan TRADOC, Manjo Janar Adamu Saliu ya bayyana cewa ya kaddamar da aikin Operation Safe Conduct kafin zaben 2019 domin tabbatar da nasara a zaben.

Labaran karya ne ke haddasa rikicin zabe - Buratai
Labaran karya ne ke haddasa rikicin zabe - Buratai
Asali: Depositphotos

Buratai ya kara da cewa ya nkuma kaddamar dad akin korafe-korafen soji wato Army Situation Room (NASR) domin lura da lamuran zaben ciki harda magance yada labaran karya.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC

Shugaban sojin yace yan ta’adda da masu tayar da kayar baya na amfani da shafukan zumunta domin yada labaran karya da gangan don haifar da rudani da kuma barkewar rikici.

Buratai ya kuma jadadda cewa babu abunda zai hana rundunar soji gudanar da ayyukanta na magance matsalolin tsaro a kasar, daidai da yadda kundin tsarin mulki ta bukata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel