PDM ta maka Al-Makura da INEC a kotun sauraron kararrakin zabe

PDM ta maka Al-Makura da INEC a kotun sauraron kararrakin zabe

- Dan takarar sanata a jihar Nasarawa na jam'iyyar PDM, Abdullahi Agwai ya shigar da Gwamna Umaru Al-Makura da INEC kara a kotun sauraron karrarakin zabe

- Agwai ya shigar da karar ne saboda hukumar INEC ba ta sanya tambarin jam'iyyarsa ba a takardan kada kuri'a da akayi amfani da shi a zaben na ranar 23 ga watan Fabrairu

- Dan takarar na PDM yana rokon kotun sauraron karar zaben ta soke zaben kuma ta bayar da umurnin a maimaita zaben bayan an saka tambarin jam'iyyarsa

Dan takarar kujerar sanatan mazabar Nasarawa ta Kudu na jam'iyyar Peoples Democratic Movement, PDM, Mr Abdullahi Agwai ya yi karar Hukumar Zabe INEC da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura wanda ya lashe zaben sanatan mazabar zuwa ofishin sauraran karar zabe da ke zamanta a Lafia.

PDM ta maka INEC da Al-Makura a kotun sauraron karar zabe
PDM ta maka INEC da Al-Makura a kotun sauraron karar zabe
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Lauya mai kare dan takarar na PDM, Christian Wanche ne ya bayyawa manema labarai hakan jim kadan bayan ya shigar da korafinsa a kan gwamnan mai barin gado a madadin wanda ya ke karewa a ranar Lahadi a garin Lafia babban birnin jihar.

Lauyan ya ce sun shigar da karar ne inda suke kallubalantar Hukumar INEC saboda cire tambarin jam'iyyar dan takararsa daga takardan kada kuri'a na zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Ya ce, "Sakamakon cire tambarin jam'iyyar wanda na ke karewa, muna rokon kotu ta soke zaben da aka gudanar a rabar 23 ga watab Fabrairu, a saka tambarin jam'iyyar sannan a maimaita zaben."

Ya kara da cewa, "Ya sabawa kundin tsarin mulki cire tambarin jam'iyya ko cire sunan dan takarar da ya cika dukkan ka'idojin shiga zabe.

"Muna sa ran za ayi mana adalci saboda an mayar da wanda na ke karewa saniyar ware a zaben."

A bangarensa, sakataren kotun sauraron karar zaben, Mr Bello Mukhtar a ya tabbatar da samun korafin na jam'iyyar PDM a hirar da ya yi da Punch. Ya ce kawo yanzu, an gabatar da kararaki hudu a gabanta daga 'yan takara daban-daban.

Mukhtar ya ce za a rufe karbar kara makonni uku bayan sanar da sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel