Wani dan Najeriya yayi kira ga tayar da masallacin Abuja bayan harin masallaci da aka kai New Zealand

Wani dan Najeriya yayi kira ga tayar da masallacin Abuja bayan harin masallaci da aka kai New Zealand

Biyo bayan mumunan harin da wani dan shekara 28 ya kai masallatai biyu a birnin Christchurch, New Zealand, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 49, wani dan Najeriya da ke amfani da shafin Twitter ya yi kira ga maimaita irin wannan harin ta’addancin babban masallacin Najeriya da ke Abuja, babbar birnin jihar.

Dan Najeriyar mai amfani da shafin Twitter dauke da suna @LegitChidi, yace ana bukatar dan ta’addan a babban masallacin Abuja.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda zai iya kalubalantar kuri’un da Buhari ya samu a Arewa - Clarke

A ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, wani shahararren dan Najeriya me amfani da shafin Twitter, Dr Joe Abah, ya wallafa wani rubutu da ke game da harin masallacin New Zealand, inda yayi kira ga yin Allah wadai da dukkanin nau’i na yan akika: addini, wariyar launin fata, akida da kuma siyasa.

Don haka yayinda sauran masu amfani da shafin Twitter ke sharhi akan rubutu sannan kuma suka yi Allah wadai da harin, sai wannan dan Najeriya, @LegitChidi, yace dan ta’addan New Zealand ya dawo babban masallacin Abuja.

“Dan Allah su dawo babban masallacin Abuja...muna bukatarsu a chan,”ya wallafa.

Abah ya kula da sharhin sannan yayi alkawarin kai rahoto ga rundunar tsaron Najeriya.

Binciken da Legit.ng tayi ya nuna cewa @LegitChidi ya sauke shafinsa na Twitter. Sai dai hoton shafinsa da aka dauka da farko ya nuna cewa a jihar Bayelsa yake da zama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel