Kone ofishin INEC: An kama 'yan sanda shida

Kone ofishin INEC: An kama 'yan sanda shida

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar kama wasu 'yan sanda shida da ake zargi da hannu cikin kone ofishin rajista na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da wasu 'yan daba su kayi a jihar Ebonyi.

Wadanda aka kama sune 'yan sandan da aka tura kula da kayan zabe na ofishin na INEC da ake karamar hukumar Ezzra ta Arewa a Jihar Ebonyi kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce an damke jami'an 'yan sandan ne saboda ba suyi wata yunkuri na hana 'yan daban kone ofishin ba duk da cewa aikinsu ne kare kayan zaben.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Kone ofishin INEC: An kama 'yan sanda shida
Kone ofishin INEC: An kama 'yan sanda shida
Asali: Twitter

'Yan daban sun kai harin ne a ofishin na INEC misalin karfe biyu na daren ranar zabe inda suka kone ofisoshi uku na hukumar dauke da muhimman kayayaki.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Awoshola Awotinde ne ya bayar da umurnin a kama 'yan sandan kamar yadda Kakakin 'yan sandan jihar, Loveth Odah ta tabbatar.

Odah ta ce kone kayayakin zaben ya janyo cikas wurin jefa kuri'a da mutane sama da 36,000 wadda hakan ya sanya dole hukumar INEC ta ce zaben bai kammalu ba.

Ta ce an tura jami'an 'yan sanda shida a kowanne cibiyan zabe.

An kuma bukaci su gaggauta sanar da hedkwatan 'yan sandan da zarar sun ga alamomin rudani ko tazarma domin a kawo musu daukin gaggawa amma ba su aikata hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel