PDP ta nemi hukumar INEC ta kaddamar da Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato

PDP ta nemi hukumar INEC ta kaddamar da Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato

A ranar Lahadin da ta gabata ne babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta nemi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC da ta kaddamar da hukuncin tabbatar da gwamna Aminu Waziri Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato.

Domin tserad da lokaci da kuma tanadin dukiya jam'iyyar adawa ta PDP a jiya Lahadi ta nemi hukumar zabe ta kasa da ta shellanta gwamna Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda ya yi nasara a yayin zaben gwamnan jihar Sakkwato da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Depositphotos

Duba da yadda ake ci gaba da kai ruwa rana tare da fuskantar matsin lamba ta fayyace wanda ya yi nasara a yayin zaben gwamnan jihar, jam'iyyar PDP ta ce hukumar INEC ba ta da wani dalili na rashin tabbatar da nasarar gwamna Tambuwal sakamakon rinjaye na yawan kuri'u da ya samu.

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, shi ne ya bayyana hakan da cewa matsayar su ba ta za ta sauya ba domin kuwa karshen tika-tika-tik ta tabbata duba da yadda sakamakon zaben ya kasance yayin da hukumar INEC ke tattara kur'i'u.

KARANTA KUMA: Sake Zabe a jihohi 6: Ba haka muka so ba, amma nasara na tare da mu

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar INEC za ta sake maimata zaben gwamna a wasu rumfuna da mazabu na jihohin Kano, Filato, Sakkwato, Adamawa da kuma Benuwe a sakamakon wasu dalilai da suka hadar da soke kuri'u.

Kwanaki biyu da suka gabata hukumar INEC ta ce ba za ta sake maimata zaben gwamna a jihohin Bauchi da Ribas ba, inda ta yanke shawarar ci gaba da tattara kuri'u da a baya tarzoma gami da tashin-tashina ta yi sanadiyar dakatar wa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel