Ci gaba ba zai taba tabbata ba a Najeriya matukar za a ci gaba da magudin zabe - Peter Obi

Ci gaba ba zai taba tabbata ba a Najeriya matukar za a ci gaba da magudin zabe - Peter Obi

Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar na ranar 23 ga watan Fabrairu, Mista Peter Obi, ya ce ba bu kasar da za ta cimma mataki na ci gaba matukar ana aikata rashin gaskiya da magudi yayin zabukan ta.

Cikin jawaban da ya gabatar a jiya Lahadi, Mista Obi ya bayyana cewa, tafarki da kuma hanyar samun shugabanci shi ne mafi a'ala ta fuskar muhimmanci a madadin rawar da kowane shugaba zai taka a bisa kujerar sa ta jagoranci.

Ci gaba ba zai taba tabbata ba a Najeriya matukar za a ci gaba da magudin zabe - Peter Obi
Ci gaba ba zai taba tabbata ba a Najeriya matukar za a ci gaba da magudin zabe - Peter Obi
Asali: Depositphotos

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Obi wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce samun kujerar jagoranci ta tsarkakakkiyar hanyar ita ce babbar madafa kuma ginshiki mai tushe na gaskiya da amana.

Ya ci gaba da cewa, aikata magudi da rashin gaskiya yayin zaben kasa na daya daga cikin mafi kololuwar nau'ikan rashin adalci da ke da babbar nasaba da rashawa mai karya duk wata garkuwa ta ci gaban kasa a siyasance da kuma tattalin arziki.

KARANTA KUMA: PDP ta nemi hukumar INEC ta kaddamar da Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato

Tsohon gwamnan ya yi tuni kan ababe na rashin gaskiyar da suka auku yayin zabukan kasar nan a bana da cewar za su yi tasirin gaske wajen cin karo da tsare-tsaren ta na dimokuradiyya da kuma gurbata makomar ta ta fuskar dakile kai wa zuwa ga Tudun tsira.

Mista Obi wanda ya jagoranci jihar Anambra tsawon shekaru takwas ya ce Najeriya ba za ta farga ba wajen gano girman ɓarna gami da ta'adin da zai hayayyafa cikin ta a sakamakon rashin adalci da miyagun ababe da suka auku a yayin babban zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel