Akwai yiwuwar INEC za ta kwace rajistar fiye da jam'iyyu 80 na Najeriya

Akwai yiwuwar INEC za ta kwace rajistar fiye da jam'iyyu 80 na Najeriya

Bisa ga tanadin doka da kuma tsari na hukuncin kundin tsarin mulkin kasar nan, akwai yiwuwar jam'iyyau goma ne kacal za su samu samu tsira wajen ci gaba da fafatawa ta fuskar gudanar da harkokin siyasa a fadin kasar nan.

Akwai yiwuwar INEC za ta kwace rajistar jam'iyyu 81 na Najeriya
Akwai yiwuwar INEC za ta kwace rajistar jam'iyyu 81 na Najeriya
Asali: Twitter

Kamar yadda shafin jaridar The Cable ya ruwaito, akwai yiwuwar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC za ta kwace rajistar kimanin jam'iyyu 81 na kasar nan a sakamakon rashin cika sharuda da kuma tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya.

A yayin da fiye da jam'iyyu 70 sun fafata wajen gudanar da harkokin su na siyasa yayin babban zaben kasa na 2019 bisa ga tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka shimfida tun a shekarar 1999, gyaran da ya auku cikin sashen sa na 225 zai tursasawa hukumar INEC kwace rajistar wasu jam'iyyun kasar nan sakamakon rashin cika sharudda da kuma tanadin tsare-tsare.

Cikin sharuddan da kuma tanadin tsare-tsare da kundin tsarin mulkin kasar na ya yi gindaya, kowace jam'iyya sai ta cika daya daga cikin bukatun hukumar INEC da suka hadar da;

- Tabbatar da cika sharuddan samun rajista daga hukumar INEC

- Ana so kowace jam'iyyu ta samu kaso 25 cikin 100 na adadin kuri'u da aka kada yayin daya daga cikin zabukan kujerar shugaban kasa ko da a jiha guda. An so kowace jam'iyya ta samu makamancin wannan kaso cikin karamar hukumar daya yayin zaben kujerar gwamna.

- Samun nasara a gunduma ko kuma unguwa guda yayin zaben shugaban karamar hukuma.

- Lashe kujera daya a zaben majalisar tarayya ko kuma majalisar dokoki ta jiha.

- Samun nasara ta lashe kujera ko da guda yayin zaben Kansila a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Ci gaba ba zai taba tabbata ba a Najeriya matukar za a ci gaba da magudin zabe - Peter Obi

Binciken manema labarai na jaridar The Cable ya tabbatar da cewa, baya ga jam'iyya mai ci ta APC da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, sauran jam'iyyu da za su samu tsira bisa ga tanadin wannan dokoki sun hadar da; APGA, YPP, AA, APM, SDP da kuma PRP.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng a jiya Lahadi ta ruwaito cewa, fitaccen Lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya shawarci hukumar INEC da ta gaggauta amfanin da karfin ikon ta wajen ribatar wannan doka domin inganta tsarin dimokuradiyyar kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel