PDP ta lashe kujeru 17, APC ta karbi 4 a majalisar jihar Benuwe

PDP ta lashe kujeru 17, APC ta karbi 4 a majalisar jihar Benuwe

Mun samu cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe kujeru 17 cikin 30 na majalisar dokokin jihar Benuwe yayin da jam'iyya mai ci ta APC ta samu nasarar kujeru hudu kacal kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kaddamar.

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Asali: Twitter

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, hukumar INEC a yau Litinin ta fayyace sakamakon zaben a ofishin ta na reshen jihar Benuwe da ke birnin Makuridi.

Kididdigar sakamakon ta zayyana cewa, a halin yanzu hukumar INEC ta kaddamar da hukuncin rashin kammalar zabe akan sauran kujeru 9 biyo bayan soke kuri'u da kuma rashin gudanar da zaben a wasu yankunan jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar INEC za ta sake zaben kujerun 'yan majalisar da hukuncin rashin kammalar zabe ya shafa tare da zaben kujerar gwamnan da za a maimata a ranar 23 ga watan Maris.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar INEC za ta kwace rajistar fiye da jam'iyyu 80 na Najeriya

Kimanin 'yan takara 432 ne suka fafata a yayin zaben kujeru 30 na 'yan majalisun dokoki na jihar, inda a halin yanzu ragowar mazabu 9 da ke ci gaba da kiradadon hukuncin sake zabe suka hadar da; Ado, Gwer East, Gboko East, Kastina-Ala West, Konshisha, Obi, Okopokwu, Otukpo da kuma Ukum.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel