Ko ku yi kwazo ko kuma mu raba gari - Obiano ya gargadi Hadiman sa

Ko ku yi kwazo ko kuma mu raba gari - Obiano ya gargadi Hadiman sa

Gwamnan jihar Anambra, Cif Willie Obiano, ya murje gashin bakin sa wajen gargadi tare da barazanar raba gari ta sawwake wa duk wani hadimin sa da ya gaza wajen jajircewa da rashin kwazo bisa aiki na nauyi da rataya a wuyan kowanen su.

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Asali: UGC

A yayin bikin murnar cikar sabuwar gwamnatin sa shekara guda na riko da akalar jagorancin jihar Anambra, Cif Obiano ya yi wannan gargadi na jan kunne da cewar dole dukanin hadiman sa da suka hadar da masu nadin mukamai da kuma kwamishinoni su jajirce wajen kwazon aiki.

Cikin jawaban sa, Gwamna Obiano ya ce dole ne dukkanin bangarorin gwamnati su jajirce ta fuskar tarayya da juna wajen aiki tukuru domin sauke nauyin da rataya wuyan su, da hakan ke da tasirin gaske a bisa mahanga ta ci gaba da bunkasar kowace jiha a fadin Najeriya.

Yayin bayyana farin ciki da kuma alfahari, gwamna Obiano ya zayyana yadda gwamnatin sa ta yi kwazon gaske wajen inganta rayuwar al'umma a jihar sa tsawon shekaru biyar da ya shafe a bisa karagar mulki.

KARANTA KUMA: PDP ta lashe kujeru 17, APC ta karbi 4 a majalisar jihar Benuwe

Duba da yadda jihar Anambra ke samun mashahuranci da kyautuwa a idanun kasashen duniya, Gwamna Obiano ya yi kira na neman hadin gwiwar dukkanin ma su ruwa da tsaki wajen fidda jihar zuwa gaci.

Da ya ke tuni na kara kaimi da kuma kwazon akan kujerar sa ta jagoranci, Obiano ya jaddada tsayuwar dakan sa wajen habaka tattalin arzikin jihar cikin tsawon shekaru uku da suka rage yayin da kuma ya ke yabawa goyon bayan al'ummar jihar sa duk da sabanin ra'ayi na siyasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel