Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zabe

Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zabe

A yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon zabe, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, ya shirya gabatar da shaidu fiye da 400 wajen shigar da korafin sa a gaban Kuliya.

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta na kujerar shugaban kasa a babban zabe da ya gudana makonni uku da su ka gabata, sun tanadi tarin shaidu domin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun daukaka kara.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku da jam'iyyar sa ta PDP na ci gaba da yin zaman dirshan kan kujerar naki ta amincewa da sakamakon zaben shugaban da hukumar INEC ta tabbatar da nasarar dan takara na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zabe
Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zabe
Asali: Facebook

A jiya Litinin cikin farfajiyar kotun daukaka kara da ke garin Abuja, Atiku da jam'iyyar PDP sun bayyana shirin su na daukar mataki domin kalubalantar sakamakon zabe da sanadin babban Lauya, Mista Emmanuel Inoidem, mashawarcin su akan harkokin shari'a.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Lauya Enoidem ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan da jam'iyyar PDP ta kammala shigar da korafin ta a gaban kotun daukaka kara da a Yammacin jiya na Litinin.

Enoidem ya yi tuni da cewa, manyan lauyoyi fiye da ashirin za su jagoranci wakilcin shigar da korafi domin kalubalantar sakamakon zabe a madadin Atiku da jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Abinda ganawar mu da shugaba Buhari ta kunsa- Sanwo Olu

A yayin da a yau Talata bayan kwanaki 21 da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, jam'iyyar PDP ta cika sharuddan shigar da korafi na kalubalantar sakamakon zabe bisa ga tanadi da kuma shimfidar dokoki na shari'a.

Ba ya ga rashin bai wa jam'iyyar PDP dama ta bincikar kayayyakin zabe kamar yadda umurnin kotu ya yi tanadi, kwarewa da sanin makamar aiki ya sanya jam'iyyar PDP ta kammala shigar da korafin ta duk da rashin samun hadin kai daga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel