Abinda ganawar mu da shugaba Buhari ta kunsa- Sanwo Olu

Abinda ganawar mu da shugaba Buhari ta kunsa- Sanwo Olu

A yau Litinin cikin fadar sa ta Villa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan Labule tare da sabon zababben gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu tare da mataimakin sa, Femi Hamzat.

Mun samu cewa a yau Litinin 18 ga watan Maris, 2019, shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin zababben gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu da kuma mataimakin sa, Femi Hamzat cikin fadar Villa da ke garin Abuja.

Abinda ganawar mu da shugaba Buhari ta kunsa- Sanwo Olu
Abinda ganawar mu da shugaba Buhari ta kunsa- Sanwo Olu
Asali: Twitter

Ganawar ta gudana ne a yayin da Sanwo Olu ya bayyana takaicin sa dangane da yadda annobar ruftawar gine-gine ke neman zama ruwan dare a jihar Legas.

KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da shugabar wata makarantar Firamare kan muzgunawa dalibai

Yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban sa dangane da dalilin ziyarar sa, Sanwo Olu ya bayyana muhimmancin taya shugaban kasa Buhari murnar samun nasarar tazarce yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun da ta gabata.

Ya ce sabuwar gwamnatin sa tun a yanzu ta daura damarar baja kolin nagartaccen jagoranci yayin riko da akalar jagoranci domin inganta jin dadi da kuma kyautatuwar rayuwar al'ummar jihar Legas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel