Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da shugabar wata makarantar Firamare kan muzgunawa dalibai

Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da shugabar wata makarantar Firamare kan muzgunawa dalibai

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da, Misis Vero Igbigwe, shugabar wata makarantar Firamare ta Okotie-Eboh da ke karkashin karamar hukumar Sapele ta jihar.

Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da shugabar wata makarantar Firamare kan muzgunawa dalibai
Gwamnatin jihar Delta ta dakatar da shugabar wata makarantar Firamare kan muzgunawa dalibai
Asali: Original

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan hukunci biyo bayan fitar wani faifan bidiyo da ya bayyana yadda ta kora wata daliba har gida, Success Adegor, a sakamakon gazawar iyayen ta na biya ma ta kudin jarrabawa.

Gwamnatin jihar ta yanke hukuncin dakatar da Misis Igbigwe yayin da kwamishinan ilimi na jihar, Barr. Chiedu Ebie ya ziyarci makarantar a safiyar yau ta Litinin.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, gwamnatin jihar ta dauki hukuncin dakatar da Misis Igbigwe a sakamakon gazawar ta na bayyana dalilai da kuma madogara ta karbar kudin jarrabawa a hannun dalibai.

KARANTA KUMA: Ko ku yi kwazo ko kuma mu raba gari - Obiano ya gargadi Hadiman sa

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai yiwuwar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC za ta rage adadin jam'iyyun siyasar kasar nan a sakamakon tanadin wata doka cikin kundin tsarin mulkin kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel