Babu wanda zai iya kalubalantar kuri’un da Buhari ya samu a Arewa - Clarke

Babu wanda zai iya kalubalantar kuri’un da Buhari ya samu a Arewa - Clarke

- Babban lauya, Robert Clarke Clarke, yace ba za a iya kalubalantar kuri’un da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu daga yankin arewa ba a kotu

- Clarke ya bayyana cewa hakan kamar tarihi ne ke maimaita kansa domin tun daga 2003 Buhari ne ke kawo yankin arewa

- Furucin nasa na zuwa ne makonni biyu bayan Atiku Abubakar ya kafa tawagar lauyoyi da za su kalubalanci sakamakon zaben Shugaban kasa da aka kammala

Wani babban lauya, Robert Clarke Clarke, yace ba za a iya kalubalantar kuri’un da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu daga yankin arewa ba a kotu.

Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris yayin da ya bayyana a wani shirin Channels TV na Politics Today.

Babban lauyan ya bayyana cewa Buhari na da tarin goyon baya daga mutannen arewa saboda abunda ya bayyana a matsayin ‘shugaban kasar ya kafa tarihi a yankin’.

Babu wanda zai iya kalubalantar kuri’un da Buhari ya samu a Arewa - Clarke
Babu wanda zai iya kalubalantar kuri’un da Buhari ya samu a Arewa - Clarke
Asali: Facebook

“Duba zaben Shugaban kasa, babu wanda zai iya kalubalanytar yawan mutanen da suka zabi shugaba Buhari a arewa saboda akwai tarihi da ya kafa a wajn.

“A 2003, Buhari ya doke kowani dan takara a arewa, a 2007 ma ya doke wani dan takara a arewa, a 2011 ya doke dukkanin yan takara a raewa, hakazalika a 2015. Don haka a 2019, idan ka duba nasarar day a samu, tarihi ya maimaita kansa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC

Furucin nasa na zuwa ne makonni biyu bayan dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar People Democratic Party (PDP), ya kafa tawagar lauyoyi da za su kalubalanci sakamakon zaben Shugaban kasa da aka kammala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel