Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC

Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC

- Wani jigon APC, Yekini Nabena, ya yi watsi da matsayar INEC kan dakatar da zaben gwamna a jihar Bauchi

- Nabena ya zargi kwamitin da Festus Okoye ke jagoranta na hukumar zaben da shirya wa jam'iyya mai mulki mugun nufi

- Kwamitin Okoye ta yi bincike akan zabe jihar sannan ta bayar da shawarar cewa za a kamala zaben ba tare da an sake zabe ba

Mataimakin babban sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yekini Nabena, ya bayyana cewa jam’iyyarsa tayi wasti da duk wani mataki da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dauka game da zaben gwamna a jihar Bauchi.

Nabena ya bayyana matsayar ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya zargi kwamitin da Festus Okeye ke jagoranta na hukumar zabe da shirya wa jum’iyya mai mulki munakisa.

Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC
Zaben gwamna a Bauchi: APC ta yi fatali da matakin INEC
Asali: Twitter

Kwamitin Okoye ta yi bincike akan zabe jihar sannan ta bayar da shawarar cewa za a kamala zaben ba tare da an sake zabe ba.

Nabea yace matsayar da INEC ta dauka ya ci karo da gyararen dokar zabe na 2010.

To sai dai a bangare guda jam'iyyar PDP wadda ke kan gaba a zaben na jihar Bauchi ta ce matakin hukumar ya yi mata daidai.

KU KARANTA KUMA: Har gobe ana aikin rashin gaskiya na na kin-karawa a Najeriya – Amurka

Jam'iyyarta bayyana haka ne duk da cewa da farko ta shigar da kara kotu ta na kalubalantar ayyana sakamakon zaben jihar a zaman wanda bai kammala ba da INEC ta yi da farko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel