APC za ta marawa Lawan da Gbajabiamila baya a takarar Majalisa

APC za ta marawa Lawan da Gbajabiamila baya a takarar Majalisa

- Ana cigaba da tseren kujerun shugabanci a Majalisar Tarayyar Najeriya

- Jam’iyyar APC tana da wadanda ta ke so su ja ragamar Majalisar kasar

- APC tana tare da Sanata Ahmad Lawan da kuma Hon. Femi Gbajabiamila

Jaridar This Day ta rahoto cewa maganar neman kujerar shugabancin majalisar tarayya yana cigaba da kara karfi. A halin yanzu dai, jam’iyyar APC mai mulki ta shiga cikin maganar inda ta ke neman fitar da ‘yan takarar ta a majalisar tarayya.

APC na yunkurin tsaida wadanda ta ke tunani su na goyon bayan jam’iyya 100-bisa-100 a matsayin shugabannin majalisar dattawa da kuma wakilan tarayya. Yin wannan da wuri shi zai bada dama APC ta kaucewa matsalar da ta shiga a 2015.

KU KARANTA: APC tace CP Singham ya taimakawa PDP wajen magudi a Kano

APC za ta marawa Lawan da Gbajabiamila baya a takarar Majalisa
APC ta na so Lawan da Gbajabiamila su zama Shugabannin Majalisa
Asali: Twitter

Manyan APC su na ta yin taro domin ganin yadda za su shawo kan lissafin majalisar kasar. Ana ganin cewa dai jam’iyyar za ta hada-kai ne ta fitar da wasu ‘yan majalisar a matsayin ‘yan takarar ta a mukamin shugabannin da za a nema.

Jam’iyyar APC za ta nemi wadanda ba za su kawowa Buhari ciwon-kai ba a matsayin shugabannin majalisar tarayya a wannan wa’adin na sa. Hakan ya sa hankalin jam’iyyar yake natsuwa da Sanata Ahmad Lawan da Hon. Femi Gbajabiamila.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa za a kai kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa Arewa ta gabas, sai kuma mataimakin sa ya fito daga cikin kudancin kasar. Shugaban wakilai kuma zai fito ne daga kasar Kudu maso yamma na Yarbawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel