Babban jigon yakin neman zaben Atiku ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Babban jigon yakin neman zaben Atiku ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Tsohon gwamnan jahar Ogun, kuma babban daraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa, Gbenga Daniel ya bayyana cewa ya kammala tattara komatsansa don fadawa jam’iyyar APC.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gbenga ya bayyana cewa ya yanke daukan wannan mataki ne sakamakon kiraye kirayen da dubun dubatan magoya bayansa suke yi masa na ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa

Babban jigon yakin neman zaben Atiku ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda
Gbenga da ATiku
Asali: UGC

Daniel ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labaru bayan kammala ganawa tsakaninsa da magoya bayansa dake fadin jahar Ogun, inda suka shaida masa cewa basu yarda ya yi murabus daga harkar siyasa ba.

Idan za’a tuna Gbenga ya bada sanarwar yin murabus daga siyasa gaba daya a ranar Asabar, inda ya bayyana haka cikin wasikar daya aika ma shugaban jam’iyyar PDP, Cif Uche Secondus, yana sanar dashi yin murabus daga jam’iyyar PDP, tare da jingine siyasa gaba daya.

Sai dai bayan kammala gawanar da yayi da magoya bayansa a Ogun, alamu sun nuna Gbenga ya sauya shawara, kamar yadda yake cewa “Kun san wannan harkace ta jagorancin al’umma, don haka muka gayyaci magoyanmu don mu ji ra’ayoyinsu.

“Dukkansu sun bayyana gamsuwarsu da murabus da nayi daga PDP, amma fa sun ce sai dai na jagorancesu zuwa jam’iyyar APC, don haka basu yarda na jingine siyasa ba, wannan shine abinda suka fada, kuma shi zamu duba.” Inji shi.

Shi dai Gbenga Daniel ya kasance gwamnan jahar Ogun daga shekarar 1999-2007 a karkashin inuwar lemar jam’iyyar PDP, kuma tun daga wancan lokaci bai taba fita daga jam’iyyar ba sai a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel