Har gobe ana aikin rashin gaskiya na na kin-karawa a Najeriya – Amurka

Har gobe ana aikin rashin gaskiya na na kin-karawa a Najeriya – Amurka

Jaridar This Day ta rahoto wani bincike da kasar Amurka tayi inda aka ce har yanzu ana tafka rashin gaskiya da barna iri-iri a Najeriya duk da yunkurin da gwamnatin Buhari take yi na yaki da barnar.

Wannan bincike da gwamnatin kasar Amurka tayi ta hannun wasu kungiyoyi masu kare hakkin al’umma da kuma damukaradiyya sun nuna cewa Buhari bai samu wata nasarar kirki wajen yakar rashin gaskiya a cikin gwamnatin kasar ba.

Binciken da Amurkar tayi ya nuna cewa ba a bin dokokin da kasa ta taada wajen hukunta wadanda ake zargi da laifi. Binciken ya kuma kara nuna cewa akwai burbushin rashin gaskiya da kama karya a kowani mataki na gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA: Abin da ya hana Kwankwaso da mutanen sa yi wa umarnin Buhari biyayya

Har gobe ana aikin rashin gaskiya na na kin-karawa a Najeriya – Amurka
Amurka tace ana barna har yanzu a Gwamnatin Najeriya
Asali: Twitter

Haka kuma an fahimci cewa hukumomin da ke yaki da barayi a kasar; ICPC da EFCC ba su yin asalin aikin su na gurfanar da masu laifi a gaban kotu har ta kai a daure masu laifi. Ana dai fama da rashin Alkalai da yawan dage kara a kotu.

Rahoton ya kuma bukaci gwamnatin kasar tayi tsauri wajen binciken dukiyar gwamnoni, da ministoci da kuma shugaban kasa da mataimakan su. Wannan zai bada dama wajen sa-ido game da arzikin ma’aikatan gwamnati a Najeriya.

Wani abin takaici kuma da binciken ya bankado shi ne yadda ake amfani da jami’an tsaro irin su ‘yan sanda da kuma sojoji wajen aikata laifuffuka a gwamnatin shugaba Buhari, ko kuma ma a kashe wasu Bayin Allah babu gaira babu dalili.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel