Ina nan daram dam dam tsundum a jam’iyyar PDP – Tsohon shugaban kasa

Ina nan daram dam dam tsundum a jam’iyyar PDP – Tsohon shugaban kasa

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton da ya dinga yawo a kafafen watsa labaru na cewa wai ya fice daga jam’iyyar PDP, sa’annan kuma yayi murabus a harkar siyasa kwata kwata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jonathan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar ta bakin kaakakinsa Ikechukwu Eze, a ranar Lahadi, inda yaceda gangan magauta suka shirya wannan rahoto don bata ma Jonathan suna.

KU KARANTA: Babu wani shugaban da aka taba yi a Najeriya dake amincewa da dokoki kamar Buhari

Ina nan daram dam dam tsundum a jam’iyyar PDP – Tsohon shugaban kasa
Jonathan
Asali: UGC

Kaakakin Jonathan ya cigaba da bayyana irin yadda PDP tayi ma Maigidansa riga da wando a siyasa, tare da zayyana irin amfanin da Goolduck Jonathan ya samu a sakamakon kasancewarsa da na haliliya ga jam’iyyar PDP.

“PDP tayi ma Jonathan komai a siyasa, ta bashi damar zama mataimakin gwamna, ya zama gwamna, ya zama mataimakin shugaban kasa har ya zama shugaban kasar Najeriya, duk a cikinta, don haka bashi da wani uzurin yin watsi da jam’iyyar a yanzu.

“Masu jin dadin watsa labaran kanzon kurege sais u daina, su rungumi wasu abubuwan da zasu fishshesu, kuma ya taimaka wajen gina Najeriya.” Inji kaakaki Ikechukwu Eze.

Daga karshe Eze ya caccaki dan jaridar daya buga labarin, inda yace sharri, kage da karya kawai yake yi ma tsohon shugaban kasa Jonathan da yace wai Jonathan ya bayyana fitarsa daga PDP ne yayin hira da kamfanin Nigeri News Agency, kamfanin da yace babu ita a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel