An kama ‘yan ta’adda uku da ake zargi da kisan DPO da wasu ‘yan sanda 3

An kama ‘yan ta’adda uku da ake zargi da kisan DPO da wasu ‘yan sanda 3

‘Yan sanda a jihar Edo sun bayyana cewar sun kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan jami’an ‘yan sanda hudu a jihar Edo.

A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda a Afuze dake karamar hukumar Owan ta gabasa a jihar Edo tare da kashe DPO da ragowar wasu ‘yan sanda uku, cikin su har da mai mukamin saja dake dauke da juna biyu.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan bindigar kimanin su 10 sun wulla wani abu fashe cikin ofishin ‘yan sandan sannan sun saka wa motocin ‘yan sanda wuta kafin daga bisani su wuce zuwa ofishin hukumar zabe dake makobataka da wurin.

An yi bajakolin masu laifin ranar Litinin a ofishin ‘yan sanda kamar yadda hadimin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar a jiya, Lahadi.

Crusoe Osagie, hadimin gwamnan, ya ce rundunar ‘yan sanda zata yiwa taron manema labarai bayanin yadda suka kai ga kama ‘yan ta’addar.

An kama ‘yan ta’adda uku da ake zargi da kisan DPO da wasu ‘yan sanda 3
Jami'an 'yan sanda
Asali: UGC

An rufe maganar ne kawai amma da gaske ne rundunar ‘yan sanda ta kama wasu daga cikin ake zargi da kai hari ofishin ‘yan sanda.

DUBA WANNAN: Abba Kyari ya bayyana abinda ya ke ci ma sa tuwo a aikin dan sanda

“Duk da mun samu labarin cewar an kama ‘yan bindigar da dama, muna fatan zamu samu Karin bayani a jawabin da kwamishinan ‘yan sandan jihar edo, Muhammed Danmallam, zai yi ga manema labarai a ranar, Litinin," a cewar Mista Osagie.

Mista Osagie ya kara da cewa gwamnatin jihar Edo zata cigaba da tabbatar da tsaron jama’ar jihar Edo da duk mazauna jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel